Isa ga babban shafi
Abu Dhabi

Nadal da Federer zasu buga wasan karshe a gasar Abu Dhabi

Federer da Rafeal Nadal
Federer da Rafeal Nadal
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

A gasar duniya ta Mubadala da ake gudanarwa a Abu Dhabi, shahararun ‘yan wasan tennis din nan na duniya guda biyu za su hadu da juna a wasan karshe na gasar, waton Rafeal Nadal dan kasar Spaniya da kuma Roger Federar na kasar SwitzerlandA wasan kusa dana karshe da aka gudanar a gasar wacce ta basu damar zuwa wasan karshe. Rafeal Nadal ne ya samu nasarar Doke Thomas Berdych dan kasar Jamhuriyyar Czech da ci 6-4 da kuma ci 6-4Sai kuma Roger Federer wanda ya doke Robin Soderling dan kasar Sweden da ci 6-7, ci 6-3 da kuma ci 6-3 a zagayen karshe.  Nadal wanda shi ne na daya a wasan Tennis a duniya, a yanzu haka zai hadu ne da Federar na biyu a wasan karshe na gasar Mubadala. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.