Wasanni

Wasan Tennis na Australia Open

Rafael Nadal
Rafael Nadal Reuters

Zamu fara labarin wasannin daga fagen da fage wasan Tennis na Australia Open dake gudana inda a gasar mata: Petra Kvitova ta doke Flavia Pennetta da ci 3-6, 6-3, da 6-3Vera Zvonareva ta doke Iveta Benesova da ci 6-4 da 6-1Agnieszka Radwanska ta doke Peng Shuai 7-5, 3-6, da 7-5Kim Clijsters ta doke Ekaterina Makarova da ci 7-6 (7/3) da 6-2 A wasannin mazaAlexandr Dolgopolov ya doke Robin Soderling da ci 1-6, 6-3, 6-1, 4-6, da 6-2Andy Murray ya doke Jurgen Melzer da ci 6-3, 6-1 da 6-1David Ferrer ya doke Milos Raonic da ci 4-6, 6-2, 6-3 da 6-4Rafael Nadal ya doke Marin Cilic da ci 6-2, 6-4 da 6-3A kwallon kafa, shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar Asia Mohamed bin Hammam, ya soki dadewar da shugaban hukumar ta duniya Sepp Blatter yayi kan madafun iko, tare da cewa haka ya janyo maganar neman karban cin hanci.Amma jami’in bai bayyana cewa ko zaiyi takarar kujerar tare da Blatter, yayin zaben watan Yuni zuwa.Ma’aikatar harkokin wasannin kasa India ta sallami manyan jami’ai biyu na kwamitin da ya tsara wasannin kasashe rainon Birtaniya, saboda gudanar da bincike game da zargin cin hanci da rashawa.Surest Kalmadi shugaban kwamitin da Lalit Bhanot sun fatattake su daga bakin aiki, domin tabbatar da gudanar da bincike.Zakarun nahiyar Turai, kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dake kasar Italiya ta sha kashi a haun kungiyar Udinese yayin wasan da aka kara jiya Lahadi, da ci uku da daya.A Ingila kungiyar Balckburn Rovers tayi nasarar doke Bromwich Albion da ci biyu da nema, yayin wasan jiya Lahadi.