wassani

Yan wassa na motsa jiki a cikin fili
Yan wassa na motsa jiki a cikin fili Reuters

Za mu somawa da bangaren ‘yan tsaren gudun fanfalaki na motoci wato Formula One.Fernando Alonso da ya kassance so 2 jere ga juna ,lambuwane ta wanan fani ,ya nuna rishin gamsuwar shi ga hukumomin kasar Espagne da su ka haranta gudun da zai wuce kilomita 110 awa,a kan manyan hanyoyin kasar.Shi kuma ya saba da dakarar hanyada gudun da ya kai kilomita dari 3 awa .Mai horar da yan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ,dan kasar Italia ,Carlo Ancelotti ya saanar da cewa ya yi mafalkin kara daga tutar kungiyar zuwa waasar garin London a hilin kwallo na Wembley.A game da wassar cin koffin gwanaye a Najeriya ,wassar karshe da ta gudana baya-baya ita ce tsakanin Bukola Babes da Ocean Boys 2da 1.Amma kuma kungiyoyi 3 da ke kan gaba sune Dolphin FC mai maki 37,sai Sunshine Stars mai mak 32 kanan Bukola Babes mai maki 30 daidai.  A game da wassar cin koffin senegal kuma Casa Sport ke gaba da maki 18.Sai us Ouakam mai maki 18 ita ma da Niary Tally mai maki 16.A karo na kusa da na kusa da na karshe ,na cin koffin France,wato Kwata final, ko kuma Kar de Finale ,kungiyar Reims da ta Nice za su karawa yau daga bakinkarfe 7 .Fatan sashen hausa ana shi ne allah ya ba mai rabo saa.