Wasanni

Wasan Polo A Lagos

Wallafawa ranar:

A wannan shirin na labarin, za mu duba shan kaye da ‘yan kasashen Nigeria da na africa ta kudu, wato Ibrahim Galadima da Danny Jordaan, da suka fito takara don wakiltar nahiya Africa a kwamtin gudanarwan hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, inda kuma suka sha kasa a zaben, inda Jacques Anouma na kasar Cote d’Ivoire da Mohamed Rouaroua na Algeria suka dare kujerun da za su wakilci nahiyar ta Africa, mutane da dama suna ganin shan kashin na dan Nigeria Ibrahim Galadima, bai rasa nasaba da lamarin nan na abin kunya kan zargin yunkurin karban na goro don zaben kasar da za ta dau nauyin wasannin kwallon kafa na duniya, da ake wa dan Nigeria nan Mr Amos Adamu.Za kuma mu leka filin kwallon dawaki wato polo, don a makon daya wuce ne aka fara wasan kwallon dawaki na shekarar 2011 a garin Lagos. Mutane da dama suna cewa wasan kwallon dawaki, wasa ne mai ban sha’awa da ake yi a kan doki, to amma sai dai a lokuta da dama in ana wannan wasan, ba kasafai za ka ga mutane sun je don kashe kwarkwatar idanun su ba, ko me ya sa? Za dai mu duba wannan a cikin shirin na yau. Wanda ni nasiruddeen Muhammad zan gabatar 

Sauran kashi-kashi