FIFA

Bin Hammam zai kara da Blatter a zaben FIFA

Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter da Mohamed Bin Hammam
Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter da Mohamed Bin Hammam

Shugaban Hukumar kwallon kafar nahiyar Asia Muhammad Bin Hammam, ya ce zai yi takara da Sepp Blatter a zaben shugabancin FIFA da za a gudanar a watan Yuni.A jawabinsa, Bin Hammam yace zai karya Blatter wanda ya kwashe shekaru 13 yana shugabancin hukumar ta FIFA.Lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kuala Lumpur, Bin Hammam yace "Sauyi ya zama wajibi, kuma ana bukatarsa," wanda zai maida hankali kan gaskiya da kuma amfani da fasahar zamani.Bin Hammam. Dai ya nemi goyon bayan kwamitin zartarwa na Hukumar kwallon kafa ta Asia domin bashi kwarin gwiwar samun nasarar lashe zaben shugaban hukumar da za’a gudanar a daya ga watan Yuni.