Manchester zata kara da Chelsea a cin kofin zakarun nahiyar Turai
Bayan fitar da kungiyoyin kwallon kafar da zasu kara da juna a wasannin Quarter Final na cin kofin Zakrun Nahiyar Turai, Manchester United ta Ingila zata kara da Abokiyar hamayyarta Chelsea.Shekaru uku da suka gabata Manchester United ce ta doke Chelsea a bugun daga kai sai gola a Moscow.Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a Spain zata kara ne da Shakhtar Donetsk ta kasar Ukrain, yayin da takwararta Real Madrid zata kara da Tottenham ta Ingila. Akwai dai yiyuwar haduwar Barcelona da Madrid a wasan kusa da na karshe idan har suka samu nasarar lashe wasanninsu a Quarter Final.Inter Milan mai rike da kambun zata kara ne da Schalke 04, kuma duk wanda ya tsallake a cikinsu shi zai kara da Manchester United ko Chelsea.
Wallafawa ranar: