FIFPro

Kwararrurn ‘yan wasan Duniya zasu taimakawa wadanda bala’i ya shafa a Japan

Dan wasan Bercelona Lionel Messi da Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Dan wasan Bercelona Lionel Messi da Cristiano Ronaldo na Real Madrid

Kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa na Duniya sun kudurta gudanar da wasa a karshen watan Mayu Domin tallafawa wadanda bala’in tsunami da girgizan kasa ta abkawa a kasar JapanKungiyar ta bayyana cewa wasar da za’a gudanar zata kunshi shahararrun ‘yan wasa da ke tashe wadanda suka hada zakaran dan wasan duniya Lionel Messi dan kasar Argentina mai taka leda a club din Bercelona da kuma Cristiano Ronaldo wanda ya yi fice a club din Real Madrid.Duk da dai kungiyar ta FIFPro bata bayyana asalin ranar gudanar da wasan ba a watan Mayu amma ta bayyana cewa tana jiran hadin kan bangaren kungiyar ta kasar Japan don tsayar da ranar gudanar da wasan.A 11 ga watan Mayu ne bala’in Tunami da girgizan kasa ta abkawa Japan, bala’in da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da Ashirin tare da raunana tashar makamin nukiliyar dake barazana ga lafiyar al’ummar kasar.