Tennis

Kim Clijsters zata kauracewa wasannin Pan Pacific Open

Kim Clijsters
Kim Clijsters rfi

Shahararriyar ‘yar wasan Tennis Kim Clijsters ta sanar da kauracewa wasannin Pacific Open da za’a gudanar a birnin Tokyo na Japan a watan Satumba saboda bala’in da kasar ke ciki musamman matsalar tashar makamashin Nuclear da ke barazana ga rayuwar al’umma.Kim Clijsters wacce ta lashe US open da Austalian Open ta kara bayyana cewa zata fice daga wasannin China Open da za’a gudanar a watan Octoba.Tuni dai a shafinta na Twitter ta mika sakwannin ta’aziya da juyayin bala’in da ya faru a kasar Japan ga ‘yan kasar