Wasanni

Ci gaba da samun 'yan Takaran Shugabancin Hukumar FIFA

Sepp Blatter Shugaban FIFA
Sepp Blatter Shugaban FIFA Reuters

Tsohon jagoran ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Chile Elias Figueroa ya yanke shawarar takarar shugabnci Hukumar Kula da Wasan Kwallo Kafa ta Duniya, FIFA, wanda za ayi a watan Yuni mai zuwa.Dan shekaru 64 da haihuwa Figueroa, sau uku yana zama kwarzon ‘yan wasan kasashen Latin Amurka a shekarun 1970, kuma yana cikin ‘yan kungiyar dake neman sauyi wa shugabancin hukumar ta FIFA.Ya zama mutun na biyu da ya nuna sha’awa kalubalantar Sepp Blatter wanda ya kwashe shekaru 13 kan mukamun. Tunda fari shugaban hukumar wasannin kwallon Nahiyar Asiya Mohamed Bin Hamman ya bayyana nasa takarar.Dan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema baya cikin masu kara wasan neman cin kofin zakarun nahiyar Turai da Tottenham, sakamakon rauni da ya samu.Benzema ya samu rauni yayin wasa wa kasarsa ta Faransa, inda aka tashi babu kare bin dazo da kasar Croacia. Ranar Alhamis ake wasan na kusa dana kusa dana karshe.Akwai yuwuwar dan wasan Barcelona Lionel Messi baya cikin masu kara wasan gaba, saboda jinyan da ya ke yi.Messi haifaffen kasar Argentina, ya na cikin wadanda ke taka rawa wa kungiyar ta kasar Spain.Dubban ‘yan kasar Indiya na ci gaba da tsallan murnar nasara doke kasra Pakistan, domin kaiwa wasan karshe na cin kofin Cricket da kasar ke daukan nauyi.An kara wasa a gaban shugabannin kasashen biyu, masu neman farfado da dangantakar kasashen. Kuma yanzu Indiya zata kara wasan karshe da kasar Sri Lanka.