wasanni

Wassar tennis ta Roland-Garros ta soma

Dinara Safina da Ana Ivanovic a wassar  Roland-Garros ta 2008.
Dinara Safina da Ana Ivanovic a wassar Roland-Garros ta 2008. (Photos : Reuters)

A yau ma an gudanar da wassa ,daga bangaren maza da na mata,dangance da kwamballar wassanin tennis ta Roland -Garros da ke gudana a kasar France.Bangaren mata zagaye na farko ga kadan daga ciki:-Espagne da Rasha 6-3 ,6-0 -Italia da Amurika 6-2,6-0Bangaren Maza Shi ma ga kadan daga ciki :-Serbiya da Jamuse 6-4,6-3,6-3-Kazakistan da Jamuse 6-2 ,6-4,6-4Shugaban hukumar kwallon kaffa ta nahiyar Asiya, Mohamed Bin Hamman da ke shirin gogawa da Josep Blatter wajen neman matsayin shugaban hukumar ta FIFA,ya furuta cewa zai kawo karshen lamarin cin hanci da karbar rashawa da ya dami hukumar .Ya yi wanan kalamai ne a game da yadda ake tuhumar hukumar da cinhanci da farbar rashawa .  Tsohon dan tseran basukur, Tyler Hamilton ya yi bayani a game da Lance Armstrong kan zargin da ake mashi na yin anfani da kwayoyi masu kara kuzari da ake tuhumar shi .Tyler Hamilton ya yi wanan bayani ne jaridar kasar Amurika US Postal. A zagayen kasar Italiya ,kilisa ta 15 a yau,ta na da nissan kilomita 230 daga garin Conegliano zuwa Gardeccia Val di Fassa.Bernard Hopkins dan kasar Amurika da ya kassance dan wassar damban zamani mafi tsofa a cikin tarihin wassar,shekaru 46 da kwanaki 126 ,ya yi galabar samun kambun duniya na masu matsakaicin nauyi a garin Montreal na kasar Canada bayan da alkalin wassa Jean Pascal ya yanke hukumci.