Japan

Tsohon dan wasan Japan Naoki Matsuda ya mutu

Naoki Matsuda Tsohon dan wasan kasar Japan
Naoki Matsuda Tsohon dan wasan kasar Japan REUTERS/Thierry Roge

Tsohon dan wasan kasar Japan , Naoki Matsuda, ya mutu a yau Alhamis sanadiyar bugun zuciya a daidai lokacin da yake gudanar da wasan motsa jiki a ranar Talata.Matsuda mai shekaru 34 na haihuwa, yana taka leda ne a club dinsa na Matsumoto Yamaga a kasar Japan.Kuma Matsuda tsohon dan wasan kasar Japan ne, kusan ya samu bugawa kasarsa wasa karo kusan 40, kuma yana cikin tawagar ‘yan wasan Japan da suka halarci gasa cin kofin Duniya da aka gudanar a hadin gwiwar kasar Japan da korea ta kudu a shekarar 2002.Tun bayan mutuwarsa ne dai magoya masoyansa a kasar Japan suka fito suna nuna juyayin mutuwarsa.