Tennis

Ba zan yi ritaya ba bayan Olympics, inji Clijsters

Kim Clijsters
Kim Clijsters RFI Hausa

Kim Clijsters Shahararriyar ‘yar wasan Tennis ta musanta jita jitar da ke cewa zata yi ritaya bayan kammala wasannin Olympics da za’a gudanar a badi a birnin London.‘Yar kasar Belgium, Kim Clijsters ta biyu a duniya a fagen Tennis tace ba wai zata yi bakwana bane bayan Olympics illa tana kokarin ganin abin da zai biyo baya bayan kammala gasar.Clijsters tace yana da wuya ta tantance wata gasa da zata kasance ta karshe a rayuwarta.