Ingila

Rikicin Birtaniya ya hana gudanar da wasa tsakanin Ingila da Holland

'yan wasan Ingila: Emile Heskey tare da Wayne Rooney .
'yan wasan Ingila: Emile Heskey tare da Wayne Rooney . Reuters

An soke gudanar da Wasan sada zumunci da aka shirya gudanarwa a gobe Laraba tsakanin Ingila da kasar Holland bisa rikicin da ke ci gaba da bazuwa a sassan yankunan Birtaniya.Hukumar kula da kwallon kafa a Ingila ce dai ta bada sanarwar dage wasar bayan ganawa da ‘yan Sanda dangane da sha’anin da ya shafi tsaro a filin wasa na Wembley da aka shirya gudanar da wasan a gobe Laraba. Akwai dai wasanni da dama da aka dage sakamakon rikicin na birtaniya.