Barcelona-Arsenal

Barcelona ta kammala cinikin Cesc Fabregas

Cesc Fabregas sabon dan wasan Barcelona
Cesc Fabregas sabon dan wasan Barcelona Reuters

Shafin Internet na Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya bada sanarwar tabbatar da kammala cinikin dan wasan Arsenal Cesc Fabregas a yarjejeniyar shekaru biyar da Barcelona.Tun ranar Lahadi ne Arsenal ta amince da cinikin dan wasan da Barcelona, sai a yau litinin ne bayan diba lafiyar dan wasan cinikinsa ya kawo karshe.An dai dade ana takaddama tsakanin Barcelona da Arsenal kan Fabregas, wanda ya fara rayuwarsa a Barcelona kafin ya koma Arsenal a shekarar 2003.Dan wasan dai ya kwashe kusan shekaru 8 yana bugawa Arsenal wasa tare da zura kwallaye 57 a raga. Fabregas dai shi ne jagoran ‘yan wasan Arsenal. Tuni kuma Arsenal ta jinjina masa tare da masa fatar Alferi a Barcelona.