Senegal

Diack na Senegal ya sake lashe shugabancin Huumar Guje Guje ta Duniya

Lamine Diack Shugaban Hukumar kula da wasanni Guje Guje ta IAAF
Lamine Diack Shugaban Hukumar kula da wasanni Guje Guje ta IAAF Ian Walton/Getty Images for IAAF

Da gagarumin rinjaye aka sake zaben Lamine Diack dan kasar Senegal, a matsyain shugaban hukumar kula da wasannin guje guje da tsalle tsalle ta duniya, amma mataimakinsa Sergei Bubka, yana bukatar lashe zagaye na biyu, kafin ya kai labari.Bubka dan kasar Ukraine yanzu haka zai sake fuskantar zabe amma wanda za ayi da hanu saboda matsalolin da na’urorin suka haifar, kuma ana gudanar da zaben a kasar Koriya ta Kudu. Magujin kasar Afrika ta Kudu mai-kafafun roba, Oscar Pistorious, zai zama gurgu na farko da zai fafata da masu kafafu cikin gasar duniya, a wani lokaci cikin wannan wata.Dan shekaru 24 da haihuwa, kasar ta Afrika ta Kudu ta zabe shi, domin shiga wasannin guje guje da tsalle tsalle da birnin Daegu na kasar Koriya ta Kudu zai dauki nauyi.Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Nahiyar Turai, UEFA, ta bayyana cewa jagoran ‘yan wasan kasar Amurka, Carlos Bocanegra, yana da damar buga wasan Europa wa kungiyar Rangers, duk da adawa da abokan karawarsu Maribor ke yi.Akwai tantama kan kammala yarjejeniyar komawar dan wasan zuwa Kungiyar Rangers daga Saint-Étienne ta kasar Faransa.