Seria A

Diego Forlan, zai koma Inter daga Atletico Madrid

Diego Forlánlokacin da yake bugawa kasarsa wasa a gasar Copa Amerika
Diego Forlánlokacin da yake bugawa kasarsa wasa a gasar Copa Amerika Reuters

Diego Forlan zai koma Inter Milan bayan Atletico Madrid ta amince ta sayarwa Inter da dan wasan.Forlan dai zai maye gurbin dan wasan kasar Kamaru ne Samuel Eto'o wanda ya bar Inter Milan zuwa club din Anzhi Makhachkala na Rasha.Forlan, shi ne aka ba kyautar zakaran dan wasa a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Africa ta kudu a bara bayan da kasarsa Uruguay ta samu kai wa zagayen kusa da na karshe.Diago Forlan dai ya kwashe shekaru 4 yana takawa club Atletico Madrid Leda wanda ya taimaka club din ya samu nasarar lashe kofin Europa na 2010 da kuma Supercup bayan ya zira kwallaye 2 a raga a wasan karshe na Europa.