Angola ta lashe gasar kwallon kwando ta mata
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan Matan Angola sun samu nasarar lashe gasar kwallon kwando ta mata bayan sun doke ‘yan wasan kasar Senegal, wanda hakan kuma ya basu damar wakiltar Africa a wasannin Olypics da za’a gudanar a birnin London.Wannan dai shi ne karo na Farko da ‘yan matan Angola suka samu damar shiga buga wasannin Olympics. ‘Yar kasar Angola ce Nassecela Mauricio aka bai wa kyautar zakarar ‘yar wasan kwallon kwandon Matan Africa.Kasar Mali mai masaukin Baki ta samu nasarar doke Najeriya a wasan neman na uku bayan ta sha kashi hannun Angola a wasan Semi Final.Yanzu haka kuma kasar Mali da Senegal zasu shiga wasannin neman zuwa wasannin Olympics tsakanin sauran kasashen Duniya bayan sun zo na biyu da na uku.