Spain

An haramtawa Mourinho shiga wasanni biyu a spain

Jose Mourinho na Real Madrid yana hada hannu da Pep Guardiola na Barcelona lokacin gudanar da wasannin Champions league.
Jose Mourinho na Real Madrid yana hada hannu da Pep Guardiola na Barcelona lokacin gudanar da wasannin Champions league. REUTERS/Felix Ordonez

Kwamaitin da’a na hukumar kwallon kafar kasar Spaniya ya haramtawa Mourinho kocin Real Madrid shiga wasanni biyu tare da cin sa tarar kudi dala 800 bisa laifin tsokane idon mataimakin kocin Bercelona lokacin wasan cin kofin Spanish Cup da aka gudanar a watan Augusta.haka ma mataimakin Kocin na Barcelona Vilanova an haramta masa shiga wasa daya saboda biye wa mourinho.Sai dai wannan dakatarwar bata shafi wasannin La liga ba ko kuma gasar kofin Copa del Ray.