Najeriya ta Fice, Nijar ta samu shiga gasar CAN 2012

Sauti 10:00
'Yan wasan Mena na Jamhuriyyar Niger
'Yan wasan Mena na Jamhuriyyar Niger @Reuters

Angola da Ghana da Guinea da Libya da Mali da Tunisia da Zambia da Code d’Ivoire da kuma Jamhuriyyar Niger ne suka tsallake zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirca bayan kammala wasannin neman shiga gasar A karshen mako.Za’a yi gasar ne ba tare da kasar Masar ba mai rike da kofin da kuma Nigeria da kasar Kamaru bayan kasa tsallakewa.Yanzu haka kasar Africa ta kudu ta garzaya domin mika kokenta ga hukumar CAF akan tsarin nan na kai-da-kai wanda ya bai wa kasar Jamhuriyyar Niger nasara.Bayan amfani da tsarin ne Niger ta samu nasara da maki 6 yayin da kuma kasar Africa ta kudu da Saliyo suka samu maki 5 bayan sun yi kunnen doki ne babu ci tsakaninsu a wasan karshe.Kasar Libya kuma ta taka rawar gani duk da rikicin da ake yi a cikin kasar, wasa daya ce suka samu bugawa a cikin kasar, sauran kuma a kasar Mali ne da Masar aka gudanar da sauran wasannin.Daga bisani an bayyana kasar Sudan da Marroco a matsayin kasashe na karshe da suka samu tsallakewa a gasar duk da cewa kasar Ghana ta lallasa Sudan ci 2 da nema, amma ta samu nasarar shiga gasar ne a tsarin kasashen da suka zo na biyu a rukuninsu masu yawan maki.