NBA

An dage gasar kwallon kwando tsawon mako biyu a Amurka

Dan wasan kwallo kwando a Amurka
Dan wasan kwallo kwando a Amurka RFI

Bayan kwashe sa’o’I goma sha uku ba tare da cim ma matsaya ba domin kokarin sasanta al’amurra a wasannin kwallon kwando a Amruka, Komishinan wasannin David Stern ya bada sanarwar dakatar da gudanar da wasannin kakar bana har zuwa tsawon makwanni biyu.An dai kwashe ‘sa’oin ne domin daidaitawa tsakanin ‘yan wasa da kungiyoyin kwallon kwandon, amma ba tare da cim ma muhimman batutuwan da ake takaddama akai ba da suka hada da kudaden haraji da kuma Karin kudaden albashi.