Barcelona

Messi zai kafa tarihi a Barcelona

L'Argentin Lionel Messi va découvrir le Milan AC.
L'Argentin Lionel Messi va découvrir le Milan AC. REUTERS/Gustau Nacarino

Lionel Messi zai kasance dan wasa na biyu a Bacelona wanda ke da yawan kwallaye a raga idan har ya zira kwallo daya a wasan ranar Assabar tsakanin Barcelona da Racing santander.Messi na bukatar kwallon daya ne kacal ya doke Kubala dan kasar Hungry daya zira kwallaye 194 a Barcelona. Kubala ya bugawa Barcelona kwallon karshe a ranar 30 ga watan Augustan shekarar 1961. Kubala shi ne magoya bayan Barcelona suka zaba a matsayin dan wasa a Barcelona lokacin da kungiyar kwallon kafar ke bukin cika shekaru 100 da kafawa a shekarar 1999.