Boxing

David Haye ya yi murabus

David Haye dan Damben Boxing
David Haye dan Damben Boxing

Dan wasan Damben Boxing David Haye tsohon zakaran ajin masu nauyi ya tabbatar da yin murabus dinsa daga shiga harakar damben na Boxing.A jiya Alhamis ne David Haye ya cika shekara 31 na haihuwa, tuni kuma ya bayyana cewa zai yi murabus a ranar da ya cika shekaru 31, kuma hakan ta tabbata idan har ba zai yi amai ya lashe ba.Haye kuma ya yi watsi da jitar jitar da ke cewa sai ya dauki fansa tsakaninsa da Vitali Klitschko wanda ya maye gurbinsa a matsayin na daya a duniya.