Tennis
Andy Murray ya lashe gasar Shanghai Masters
Wallafawa ranar:
Andy Murray na Birtaniya ya lashe gasar Shanghai Masters bayan ya doke David Ferrer na Spaniya a wasan karshe da aka gudanar.Wannan ita ce nasara ta uku da Murray ke samu a cikin dan lokaci bayan ya lashe gasar a Bangkok da Tokyo da kuma wannan nasarar ta Shanghai Masters.Wannan nasarar ce kuma tasa Andy Murray ya maye gurbin Roger Federer a matsayin zakaran Tennis na Duniya.