FIFA

Jack Warner ya zargi Blatter na FIFA

Jack Warner Tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Zurich  30 mayu 2011.
Jack Warner Tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Zurich 30 mayu 2011. REUTERS/Arnd Wiegmann

A wata wasika da ya aikawa jaridar Gurdian ta Trinidad Tsohon shugaban hukumar FIFA Jack Warner ya fallasa wasu bayanai akan shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter.Mista Warner na daya daga cikin wadanda hukumar FIFA ta dakatar tare da Bin Hamman a watan Juni a wata badakalar cin hanci da rashawa wajen yakin neman zaben Bin Hamman da ke hamayya da Blatter.Mista Warner a wasikar day a rubuta, yace Blatter ya yi amfani da shi da Bin Hamman domin bada tsoshiyar baki a yakin neman zabensa a shekarar 1998 da 2002.