Barcelona

Guardiola ya jinjinawa Iniesta

Xavi, ya rungume  Iniesta tare da  Messi
Xavi, ya rungume Iniesta tare da Messi AFP

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya jinjinawa dan wasansa Andres Iniesta a matsayin wani dodon wasa bayan kwashe lokaci Messi na haskawa.Cikin mintina 10 da fara wasa ne Iniesta ya zira kwallo a raga bayan sun yi musayar kwallo da Messi a wasan gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai tsakanin Barcelona da Viktoria Plzen.A cewar Guardiola duk da cewa Messi na tashensa, amma Iniesta dan wasa ne idan yana fili Barcelona bata da shakku.