Tennis

Kvitova ta doke Wozniacki a Istanbul

Wozniacki
Wozniacki AFP

Caroline Wozniacki Shahararriyar ‘Yar wasan Tennis ta daya a duniya ta sha kashi hannun Petra Kvitova a gasar Tennis da duniya da ake gudanarwa a kasar Turkey.Wozniacki ‘Yar kasar Denmark mai shekaru 21 na haihuwa wannan ne karo na biyu da aka samu galabarta bayan buga wasanni 80 a kakar wasar bana.A daya bangaren kuma Victoria Azarenka ta Belarus ta nemi tsallakewa zuwa buga wasan Semi Final bayan ta doke Li Na ‘yar kasar China.