Cricket

Kotu ta yanke hukuncin dauri ga ‘yan wasan Pakistan na Cricket

'Yan wasan Pakistan Muhammad Asif da Salman Butt
'Yan wasan Pakistan Muhammad Asif da Salman Butt Reuters/Philip Brown

A yau Alhamis wata kotun Birtaniya ta yankewa ‘yan wasan Cricket na Pakistan hukuncin dauri a gidan yari bayan kama su da laifin yunkurin yin coge a wasa tsakanin Pakistan da Ingila.Wakilin wasan cricket Majeed, wanda ya shiga tsakani, kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 2 da wata takwas.Tsohon jagoran ‘yan wasan Pakistan Salman Butt an yanke masa hukuncin daurin watanni 30, Muhammad Asif kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekara daya sai karaminsu Muhammad Amir mai shekaru 19 aka yanke masa hukuncin watanni shida.