Ingila

Tevez zai sake fuskantar Fushin Manchester City

Carloz Tévez dan wasan Manchester City cikin motarsa bayan kammala wasa a Bayern Munich
Carloz Tévez dan wasan Manchester City cikin motarsa bayan kammala wasa a Bayern Munich © Reuters

Carlos Tevez zai sake fuskantar fushin Manchester City bayan dan wasan yaki dawowa horo a jiya Laraba.Yanzu haka Kungiyar Manchester City ta bukaci lauyoyinta su dauki mataki akan Carlos Tevez. Kungiyar  ta zira ido ne tana jiran Tevez ya dawo horo amma a ranar Talata rahotanni suka nuna cewa yana Argentina.Wannan takaddamar ta samo asali tun bayan da dan wasan yaki bugawa City wasa tsakaninta da Bayern Munich a gasar cin kofin zakrun Turai.