Najeriya

Keshi ya sha alwashin sharewa ‘Yan Najeriya hawaye

Stephen Keshi lokacin da yake aikin horar da 'yan wasan Togo
Stephen Keshi lokacin da yake aikin horar da 'yan wasan Togo

Sabon kocin Super Eagle Stepehn Keshi, ya yi alkawalin sharewa ‘Yan Najeriya hawaye, inda zai fara aikin shi da wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Boswana da kuma kasar Zambia.Yanzu haka dai Keshi ya kira mai tsaron Gidan Lille ta Faransa Vicent Enyeama da dan wasan Fulham Diskson Etuhu, tare da gayyatar dan wasan Wigan a karon farko Victor Moses a wasan da Nigeria zata kara da Boswana.Sai dai Super Eagle zasu buga wasan ne ba tare da dan wasan Westbrom ba Osaze Odemwingie.Wasu dai suna ganin babu wani sauyi a Tawagar Keshi sabanin Tawagar Siasia.