Tunisia

Esperance ta lashe gasar Zakarun Africa

'yan wasan Esperance lokacin da suke murnan zira kwallon Harrison Afful.
'yan wasan Esperance lokacin da suke murnan zira kwallon Harrison Afful. REUTERS/Zoubeir Souissi

Kungiyar kwallon kafa ta Esperance ta Tunisia ce ta lashe gasar cin kofin zakarun Africa bayan ta doke Wydad Casablanca ta morocco da ci daya mai ban haushi.Dan kasar Ghana ne Harison Afful ya zirawa Esperence kwallonta daya da ya bata wannan nasarar, bayan buga wasan farko a kasar Morroco gidan Wydad ba tare da zira kwallon a raga ba.Yanzu haka kuma asusun bankin Esperence ya cika ya tunbatsa da kyautar kudi dala miliyan daya da rabi. Esperence kuma ita ce zata wakilci Africa a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa da za’a gudanar a Japan a watan Gobe inda akwai yiyuwar zata iya karawa da Barcelona.Ko a bara Esperence ce ta buga wasan karshe tsakaninta da TP Mazembe ta Jamhuriyyar Demokradiyar Congo kungiyar kwallon kafa ta farko daga Africa da ta buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa duk da cewa ta sha kashi hannun Inter Milan ci 3-0.