Champions League

Arsenal ta tsallake, Chelsea ta sha kashi hannun Leverkusen

Van Persie wanda ya zira Arsenal Kwallayenta
Van Persie wanda ya zira Arsenal Kwallayenta

Chelsea bata sha dadi ba a wasannin champion League da aka gudanar a ranar laraba, domin Bayer Leverkusen ta doke ta ci 2-1. Mai horar da ‘yan wasan na Chelsea Andre Villas-Boas yana fuskantar kalubale yanzu haka, domin wannan ne karo na hudu da Chelsea ke shan kashi cikin wasanni bakwai. 

Talla

Kafin Chelsea ta tsallake sai ta doke Valencia a Stamford Bridge, inda Valencia kuma ta doke Genk ci 7-0. Saldado ne ya zira kwallaye uku a raga.

Arsenal kuma ta tsallake bayan da ta doke Borussia Dortmund, ci 2-1. Robin Van Persie ne ya zirawa Arsenal kwallayenta biyu.

A Faransa kuma Olympic Marseille ta sha kashi ne hannun Olympiakos ta Girka.

Marseille ce ke bi ma Arsenal a Rukuninsu, maki daya tsakaninta da Olympiakos, Amma a wasan karshe Borussia Dortmund ce zata karbi bakuncin Marseille, Arsenal kuma ta kai wa Olympiakos ziyara.

A filin wasa na San siro kuma Bercelona ta doke AC Milan ci 3-2.
Barcelona da AC Milan tun a wasannin da suka gabata ne suk tsallake.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.