Boxing

Vitali Klitschko ya amince da bukatar Haye domin fada da juna

Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing  Rike da kyautar da ya lashe a Barlin kasar Jamus
Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing Rike da kyautar da ya lashe a Barlin kasar Jamus REUTERS/Tobias Schwar

Tsohon zakaran Damben Boxing David Haye wanda ya yi amai ya lashe bayan bayyana yin ritaya, yanzu haka Vitali Klitschko ya amince da bukatarsa na yin fada da juna.

Talla

Wakilan Vitali da Vladimir Klitschko ‘yan uwan Juna ‘yan kasar Ukrain sun shaidawa kamfanin Dillacin labaran Reuters amincewarsu da bukatar David Haye na fitowa fadan Kece Raini.

A watan Yuni ne Vladimir Klitschko ya doke David Haye a Damben Boxing Ajin masu nauyi, kuma a ranar bukin haihuwarsa ne 31 ga watan Octoba Haye ya bayyana yin Murabus.

A ranar Litinin ne Haye yace zai dawo idan har Vitali ya amince ya yi fada da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.