Rukunin gasar Turai, amma an yi waje da Najeriya zuwa Olympics

Sauti 09:56
Taambarin kwallon kafa da aka kirga a ranar bukin hada rukunin gasar Turai a birnin Kiev
Taambarin kwallon kafa da aka kirga a ranar bukin hada rukunin gasar Turai a birnin Kiev Reuters/Kacper Pempel

A cikin shirin mun diba rukunin kasashen da zasu kara da juna a gasar cin kofin nahiyar Turai da za’a gudanar a badi, bayan fitar da rukunin a karshen makon jiya, sannan kuma muka leka Africa domin jin yadda aka yi waje da Najeriya a wasannin kwallon kafa na neman shiga Olympics da ake gudanarwa a kasar Morroco. Bayan kasa tsallakewa shiga gasar cin kofin Africa.

Talla

A badi ne dai za’a gudanar da gasar cin kofin Turai, kuma kasashen ukrain ne da Poland zasu dauki nauyin gudanar da gasar, inda kasashe 16 zasu halarci gasar domin karawa da juna.

To a karshen makon jiya ne aka hada kasashen da zasu kara da juna zuwa rukuni 4 wato ABC zuwa D, domin karawa a zagyen farko

A rukunin A an hada kasar Poland ne daya daga cikin wadda zata dauki nauyin gasar tsakaninta da kasar Girka da Rasha da kuma Jamhuriyyar Czech.

A rukunin B kuma aka hada kasar Holland da Denmark da Jamus da Portugal

Sai rukunin C kuma Spain mai rike da kofin aka hada ta tsakaninta da kasar Italiya da taba lashe kofin a shekarar 1968 da kuma Jamuhuriyyar Ireland da Croatia.

A rukunin karshe kuma na D an hada kasar Ingila ne da bata taba lashe kofin ba tsakaninta da kasar Faransa da ta taba lashe kofin koro biyu, sai kuma kasar Ukraine da zata dauki nauyin gasar da kuma kasar Sweden.

Al amin Idris yahaya wani masoyi kwallon kafar Turai ne ya muna nazari dangane da wadannan rukunin kasashe da aka fitar.

To a bana dai wasan kwallon kafa ba ta yi wa Nigeria dadi ba domin a badi za’a buga wasannin ne ba tare da ‘yan wasanta ba,

Akwai gasar cin kofin Africa da za’a gudanar a watan Janairun badi ba tare da ‘yan wasan Super Eagle ba, haka ma wasannin Olypics an yi waje da ‘yan matan Falcons ga kuma tawagar Austine Eguaboen.

Akan haka kuma shirin ya tattauna da Sani Toro tsohon Sakatare Janar na hukumar kwallon kafa a Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI