FIFA

Messi, Ronaldo ko Xavi FIFA zata zaba gwarzonta

Leo Messi dan Wasan Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid
Leo Messi dan Wasan Barcelona da Cristiano Ronaldo na Real Madrid

Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo da Xavi hukuamar FIFA ta kebe matsayin wadanda zasu iya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya.

Talla

Messi dan wasan Barcelona mai shekaru 24 na haihuwa shi ke rike da kambun, kuma akwai yiyuwar zai iya lashe kyautar ta bana karo uku a jere bayan ya lashe a bara da kuma shekara ta 2009.

A kakar wasan bana ne Messi ya kafa tarihin zirawa Barcelona kwallaye 200, inda yake kokarin cim Ceser Rodriguez' wanda ya zirawa Barcelona kwallaye 235 kuma wanda ya fi kowa zira kwallaye a raga a tarihin Barcelona.

Dan wasan Real Madrid kuma Cristiano Ronaldo mai shekaru 26 ya taba lashe kyautar a shekarar 2008, kuma so biyu yana zuwa matsayi na biyu a shekarar 2007 da 2009.

Sai kuma Xavi Hanandez na Barcelona wanda a bara ma yana cikin ‘yan wasa uku da FIFA ta kebe domin zaba gwazonta.

Akwai dan wasan Manchester United Wayne Rooney da aka zaba domin tantance kwallon daya fi shahara a cikin raga bisa wata kwallo daya zira ta sama a ragar Manchester City a bara.

Daga cikin masu horar da ‘yan wasa kuma FIFA ta kebe kocin Manchester United Sir Alex Farguson da kocin Barcelona Pep gurdiola da abokin hamayyarsa a La liga kocin Madrid Jose Mourinho.

Cikin mata kuma an kebe ‘yar wasan Brazil Marta wacce ta lashe kyautar karo biyar sai kuma jar wasan Japan Homare Sawa da kuma ‘yar wasan kasar Amurka Abby Wambach,

‘Yan jaridu ne da masu horar da ‘yan wasa da jagoran ‘yan wasan kasashe ke kada kuri’ar zaben gwarzaye a fagen kwallon kafa.

A ranar 9 a watan Janairu ne za’a fitar da gwani a birnin Zurich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.