Kwallon Kwando

An kawo karshen rikicin wasannin kwallon kwando a Amurka

'Yan wasan Los Angeles Lakers na Amurka
'Yan wasan Los Angeles Lakers na Amurka REUTERS/Mike Stone

A yau ne za’a bude wasannin kwallon kwando a kasar Amurka bayan kwashe tsawon watanni biyar da dakatar da gudanar da wasannin. Saboda sabani tsakanin ‘yan wasa da kungiyoyin kwallon kwandon.

Talla

A jiya alhamis ne dai aka cim ma matsaya tare da amincewa da wata sabuwar yarjejeniya ta shekaru 10 tsakanin kungiyar ‘yan wasan da kungiyoyin kwallon kwandon.

Ana tunanin bude wasannin a lokacin bukin kirsimeti inda Los Angeles Lakers zata karbi bakuncin Chicago Bulls, sai kuma Dallas ta kara da Miami.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.