Faransa

Benzema ya samu kyautar gwarzon dan wasan Faransa

Karim Benzema a lokacin da ya zira kwallo wasan Clasico cikin dakika 22 tsakanin Real Madrid da Barcelona
Karim Benzema a lokacin da ya zira kwallo wasan Clasico cikin dakika 22 tsakanin Real Madrid da Barcelona © Reuters

Wata mujalla a kasar Faransa ta ba Karim Benzema kyautar gwarzon dan wasan kasar na bana. Dan wasan ya samu yawan maki 155, fiye da Eric Abidal wanda ya zo na biyu da maki 110, kodayake ya taba lashe kyautar, mai tsaron gidan Lyon ne a matsayi na uku Hugo Lloris inda ya samu maki 69.

Talla

A bara da bana dai Benzema ya taka rawar gani a Real Madrid, a makon da ya gabata shi ya zira kwallo a raga cikin lokaci kankani da fara wasan El Classico tsakanin Madrid da Barcelona.

Mujallar kuma ta zabi Rudi Gercia na Lille matsayin zakaran koci wanda a karon farko ya kai Lille da samun nasarar lashe gasar league a kasar tun bayan shekarar 1954.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.