Ingila

Fletcher, Dan wasan Manchester United ya tafi hutu

Dan wasan Manchester United Darren Fletcher lokacin yake murnar zira kwallo a ragar Benfica lokacin wasan zakarun Turai.
Dan wasan Manchester United Darren Fletcher lokacin yake murnar zira kwallo a ragar Benfica lokacin wasan zakarun Turai. REUTERS/Phil Noble

Dan wasan Manchester United dan kasar Scotland Darren Fletcher ya tafi hutu na dan wani lokaci daga buga wasa saboda rashin lafiyar ciwon ciki da yake fama da ita.

Talla

Sanarwar data fito daga shafin Internet na Manchester United, an bayyana cewa dan wasan yana fama da cutar gyambon ciki ta Ulcer.

Wasan sa ta karshe ita ce wasan zakarun Turai ta champions league da United ta buga tsakaninta da Benfica inda aka ta shi ci 2-2 kuma yana daya daga cikin wadanda suka zira kwallo a raga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.