kwallon kafa

Barcelona V Santos a wasan karshe ta kungiyoyin Duniya

Dan wasan Barcelona Seydou Keita lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar  Al  Sadd.
Dan wasan Barcelona Seydou Keita lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Al Sadd. © Reuters

A gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa, Barcelona ta doke Al Sadd ta Qatar ci 4-0. inda zata kara da kungiyar Santos ta Brazil a yankin kudancin Amurka wasan karshe da za’a gudanar a ranar Lahadi.

Talla

Sai dai Mai horar da ‘yan wasan kungiyar al Sadd Jorge Fossat, yace bai damu ba ko kadan da kashin da suka sha illa Karin basira da fasahar kwallon kafa a karawarsu da Barcelona.

Kungiyar al Sadd itace ta doke Esperance ta Tunisia wacce ta wakilci Africa, amma Mista Fossati yace buga wasa da su Xavi da Fabregas abun alfahari ne.

Amma kuma a wasan Barcelona ta yi hasarar dan wasanta David Villa wanda ya kare kafar shi, Ana tunanin zai kwashe tsawon watanni biyar yana jinya.

A jiya ne Alhamis ne kuma Wata Mujallar wasanni ta duniya ta zabi dan wasan Barcelona Lionel Messi gwarzonta na Duniya tare da Pep Gurdiola matsayin zakaran koci.

Messi ya samu kashi Sittin daga kuri’un da masu Karatun Mujallar suka kada inda ya doke Cristiano Ronaldo wanda ya zo na biyu, Xavi Hanandez kuma a matsayi na uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.