CAF

Hukumar CAF ta ware 'Yan wasa uku da zata zaba gwarzonta

'Yan wasan da CAF ta ware Seydou Keita, dan kasar Mali da Dan kasar Ghana André Ayew, da  Yaya Touré na Manchester City.
'Yan wasan da CAF ta ware Seydou Keita, dan kasar Mali da Dan kasar Ghana André Ayew, da Yaya Touré na Manchester City. Reuters / montage RFI

Hukumar CAF da ke kula da kwallon kafa a Afrika ta ware ‘yan wasa uku da zata zaba gwarzon Afrika a bana, a bangaren maza da mata da gwarzon koci tare da ware kasashe uku cikinsu har da Jamhuriyyar Nijar da hukumar zata zaba kasa fitacciya a kwallon kafa. A ranar Alhamis ne CAF zata bayyana wanda zai lashe kyautar gwarzon dan wasan. 

Talla

Gwarzon dan wasa
Andre Ayew (Dan Kasar Ghana da ke wasa a Marseille/Faransa)
Seydou Keita (Dan kasar Mali da ke wasa a Barcelona/Spain)
Yaya Toure (Dan kasar Cote d’Ivoire da ke wasa a Manchester City/Ingila)

Matashin dan wasa a Afrika
Oussama Darragi (Tunisia da ke wasa a Esperance)
Zouhaier Dhaouadi (Tunisia da ke wasa a Club Africain)
Banana Yaya (Kamaru da ke wasa a Esperance)

Kasar da ta shahara a kwallon kafa a bana CAF ta ware
Botswana
Cote d’Ivoire
Nijar
Tunisia

Jaruma a bangaren Mata CAF ta ware:
(a) Nompumelelo Nyandani (Africa ta Kudu)
(b) Perpetua Nkwocha (Najeriya)
(c) Miriam Paixao Silva (Equatorial Guinea)

Cikin Alkalan wasa CAF ta ware:
(a) Alioum Neant (Kamaru)
(b) Noumandiez Doue (Cote d’Ivoire)
(c) Djamel Haimoudi (Algeria)
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI