Kwallon kafa

Beckham ba zai dawo PSG ba

David Beckham ya yi watsi da bukatar PSG na komawa bugawa kungiyar wasa a Faransa, inda yace iyalinsa ne suka yanke wannan hukuncin. Sai dai har yanzu babu tabbas ko dan wasan zai koma Amurka club dinsa na Los Angeles Galaxy, kamar yadda jaridar Los Angeles times ta ruwaito.

David Beckham Tsohon jagoran 'Yan wasan Ingila.
David Beckham Tsohon jagoran 'Yan wasan Ingila. Reuters
Talla

Babban jami’in gudanarwar kungiyar Galaxy ya shaidawa Jaridar cewa har yanzu babu wata yarjejeniya a kasa domin neman Beckham zai ci gaba da taka leda a Galaxy. Sai dai yace har yanzu suna bukatar dan wasan.

Tun a makon jiya ne kungiyar PSG ta yi ikirarin cim ma yarjejeniyar watanni 18 tsakaninta da Beckham, amma kuma shugaban kungiyar ta PSG Nasser al-Khelaifi ya shaidawa manema labarai a filin wasan Tennis a birnin Doha na kasar Qatar cewa babu wata yarjejeniya tsakanin club dinsa da David Beckham.

A ranar jajibirin sabuwar shekara ne kwangilar Beckham ta shekaru biyar ta kawo karshe da Galaxy, amma kuma kungiyoyi da dama daga ingila da Italiya da Brazil da yankin gabas ta tsakiya na neman dan wasan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI