FIFA

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Duniya karo na uku

Dan wasan Barcelona Lionel Messi lokacin da ya karbi kyautar gwarzon dan wasan duniya karo na uku a birnin Zurich
Dan wasan Barcelona Lionel Messi lokacin da ya karbi kyautar gwarzon dan wasan duniya karo na uku a birnin Zurich REUTERS/Christian Hartmann

Lionel Messi ya lashe kyautar FIFA ta gwarzon dan wasan bana karo na uku a jere, bayan ya doke abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo da abokin wasan shi Xavi Hernandez. Messi shi ne dan wasa na biyu da ya taba lashe kyautar sau uku a jere bayan shugaban EUFA Michel Platini wanda ya lashe kyautar sau uku a jere lokacin da yake taka kwallo a Juventus tsakanin shekarar 1983-85.

Talla

Kocin Barcelona ne kuma Pep Guadiola ya lashe kyautar gwarzon koci a bana. Bayan ya sha gaban Jose Mourinho na Real Madrid da Sir Alex Ferguson na Manchester United. Sai dai Sepp Blatter ya mika kyautar shugaba ga Sir alex Ferguson bisa rawar da ya taka shekaru 25 yana jagorancin United a old Trafford.

A Tawagar kungiyar FIFA kuma Bercelona da Real Madrid ne suka yi mamaya, inda FIFA ta zabi ‘yan wasan Bercelona biyar cikin kungiyarta wato Messi da Xavi da Andres Iniesta da Gerard Pique da Dani Alves.

Real Madrid kuma ta samu wakilcin ‘yan wasa guda hudu, wato Iker Casillas, Sergio Ramos, Xabi Alonso da Ronaldo

‘Yan wasan Manchester United ne guda biyu suka cika gibin tawagar ta FIFA, wato Nemanja Vidic da Wayne Rooney.

A bangaren mata kuma kasar Japan ce ta lashe kyautunan na FIFA inda Homare Sawa ta lashe kyautar jarumar ‘Yar wasa, Nario Sasaki kuma ta karbi kyautar Jarumar mai horar da ‘yan wasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI