Kwallon kafa

An cire wa Maradona duwatsu a kodar shi

Dan kasar Argentina Diego Armando Mardona kocin kungiyar Al wasl ta daular larabawa
Dan kasar Argentina Diego Armando Mardona kocin kungiyar Al wasl ta daular larabawa © Reuters/Oleg Popov

Maradona ya yi jinya a asibiti bayan yi masa tiyata inda aka cire masa wasu duwatsu a kodar shi. Maradona ya fara jin ba daidai ba ne bayan kungiyar da yake jagoranta a Daular larabawa ta Al wasl ta kammala wasa a ranar Assabar. anan take ne kuma aka garzaya da shi asibiti inda aka yi masa tiyata.

Talla

A yau litinin ne dai ake sa ran za’a sallame shi daga asibiti.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI