Scholes ya haska, Inter ta doke Milan, Real da Barca sun lashe wasanninsu
Wallafawa ranar:
A wasannin da aka gudanar karshen mako, Manchester united makin ta daya da Manchester City a Ingila, Real Madrid da Bercelona dukkaninsu sun lashe wasanninsu, Inter Milan kuma ta doke AC Milan. Ancelotti ya lashe wasan shi ta farko a PSG.
Ingila
A Ingila dai yanzu makin Manchester United daya ne da Manchester City a saman Table bayan United ta doke Bolton ci 3-0, Kafin City ta buga wasanta a yau Litinin.
Paul Scholes dan wasan United ya samu nasarar zira kwallo a ragar bayan dawowa fagen wasa.
Tottenham kuma ta yi kunnen doki ne ci 1-1 tsakaninta Wolves.
Arsenal ta sha kashi ne hannun Swansea City ci 3-2.
Chelsea kuma ta samu nasarar doke Sunderland ci 1-0 a Stamford Bridge.
Spain
A La liga kuma Bercelona ta doke Real Betis ci 4-2, wannan nasarar ce ta datse yawan maki 8 zuwa 5 da Real Madrid ta ba Barcelona a ranar Assabar bayan Madrid ta samu nasarar Doke Mallorca ci 2-1.
Italiya
A gasar Seria A, Inter Milan ta samu nasarar doke AC Milan ci 1-0 a filin wasa na San Siro.
Dan kasar Argentina ne Diego Milito ya zirawa Inter kwallonta a ragar Milan, kuma yanzu Inter ta gurguso zuwa matsayi na biyar a saman Table maki 5 tsakaninta da AC Milan.
A daya bangaren kuna Juventus ta yi kunnen doki ne ci 1-1 tsakaninta da Caglairi
Faransa
A French League, Marseille ta lallasa Lille ci 2-0, kuma wannan ne karo na farko da aka samu galabar Lille bayan buga wasanni goma sha bakwai ba tare da samun galabarta ba.
A ranar Assabar kuma Carlo Ancelotti ya lashe wasan shi ta farko a PSG bayan ya doke Toulouse ci 3-1, kuma yanzu PSG ce ke jagoranci table da yawan maki 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu