Kwallon kafa

Barcelona ta yi waje da Madrid a Copa del Ray

Messi rike da kwallo a kafar shi Pepe na Madrid na biye da shi.
Messi rike da kwallo a kafar shi Pepe na Madrid na biye da shi. REUTERS/Susana Vera

A wasan Clasico tsakanin Barcelona da Madrid an tashi ne ci 2-2 a gasar Copa del Ray, sai dai Bercelona ta yi waje da Madrid bayan ta doke ta ci 2-1 a Bernabeu. Jose Mourinho har yanzu bai samu galabar Barcelona a gidanta ba cikin wasannin 9 daya yake bugawa a Madrid da wata kungiya da ya jogaranta.

Talla

Kafin kammala wasan Sagio Ramos na Madrid ya karbi jan kati. Da farko kuma Barcelona ce ta fara zira kwallaye biyu a raga kafin Cristiano Ronaldo da Karim Benzema su barkewa Madrid kwallayen.

A yau ne kuma Velencia zata kara da Lavente kuma tsakaninsu ne Barcelona zata kara da wanda ya doke wani.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI