Marseille da Lyon zasu kece raini kafin wasan karshe a French Cup
Marseille da Lyon da suka tsallake zuwa wasan karshe a gasar French Cup, a ranar lahadi ne zasu fara kece raini da juna a gasar cin kofin League inda dukkaninsu ke neman gurbin shiga gasar zakarun Turai.
Wallafawa ranar:
Marseille tana a matsayi na biyar ne a saman Table, maki biyu ya rage ta tsallaka gurbin shiga gasar zakarun Turai, Lyon kuma tana mastayi na hudu ne amma kowannensu zai yi fatar doke wani domin haurawa saman Table.
A gobe Assabar ne kuma Paris Saint-Germain da ke Jagorancin Table maki uku tsakaninta da Montpellier, zata haska sabbin ‘yan wasanta Alex na Brazil da Thiago Motta a wasan da zata karbi bakuncin Evian.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu