FIFA

FIFA zata bada tallafin kudi ga ‘Yan uwan wadanda suka mutu a Masar

Shugaban Hukumar FIFA  Sepp Blatter lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Tokyo bayan kammala taronsu  shugabannin hukumar
Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Tokyo bayan kammala taronsu shugabannin hukumar Reuters/Kim Kyung-Hoon

Hukumar kwallon kafa ta FiFa ta yi kira ga hukumomin kwallon kafa a duniya domin tallafawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a rikicin kwallon kafar kasar Masar, FIFA tace zata bada tallafi ga ‘yan uwan mamatan Dala 250,000, a rikicin kwallon kafar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 70 a makon jiya.

Talla

FIFA tace zata biya kudaden ne ta hanyar asusun tallafi na kungiyar Al Ahly da rikicin ya shafa tsakanin magoyanta da kungiyar Al masry.

Tun aukuwar al’amarin ne Sepp Blatter shugaban hukumar ta FIFA ya bayyana cewa wannnan rikicin rana ce ta bakin ciki ga kwallon kafa

Akan haka ne kuma yace ya zama dole FIFA ta tallafa da sauran hukumomin kwallon kafa a kasashen duniya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.