Kwallon kafa

Pele na Brazil yace babu wani Pele sai shi

Tsohon dan wasan Brazil Pele yana sumbatar mutum mutumin shi kusa da shugaban kasar Gabon Ali Bongo  a wajen harabar filin wasa a birnin Libreville
Tsohon dan wasan Brazil Pele yana sumbatar mutum mutumin shi kusa da shugaban kasar Gabon Ali Bongo a wajen harabar filin wasa a birnin Libreville REUTERS/Thomas Mukoya

Mazan jiya tsohon dan wasan Brazil Pele ya jaddada cewa ba wani Pele sai shi, a lokacin da ake bukin girke mutum mutumin shi a filin wasan da za’a buga wasan karshe ta gasar cin kofin Afrika a birnin Libreville.

Talla

A lokacin Bukin, cikin taron mutane cikin raha, shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya jefa tambaya cewa ko, wane dan wasa ne ya sha gaban Pele? sai Pele ya kada baki yace haihuwar wani Pele yana da wahala, wata kila a samu dan wasa kwatankwacin Pele, amma samun wani Pele abu ne mai wahala saboda iyayen shi sun kammala kirar Pele kuma injinin buga Pele ya yi gama aiki.

Tarihi ne dai ya tuna Pele a kasar Gabon inda sanadiyar shi aka kawo karshen yaki a kasar, inda a zamanin shugaban kasa a lokacin Umar Bongo mahaifin Ali Bongo, yace zasu kawo karshen yaki saboda suna son yin ido biyu da Pele, kuma hakan ta faru, sanadiyar Pele aka kawo karshe yaki a lokacin.

Lokacin kuma Pele suna Ziyara ne Afrika cikin tawagar kungiyar shi ta Santos inda suka buga wasa a da Gabon da Zaire a shekarar 1967.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.