Premier

Suarez zai sake karawa da Evra a Premier

Dan wasan Liverpool Luis Suarez a gefen hagu tare dan wasan Manchester United Patrice Evra suna kallon juna a lokacin wasan Premier a filin wasa na Anfield. lokacin da Evra yace Suarez ya zage shi
Dan wasan Liverpool Luis Suarez a gefen hagu tare dan wasan Manchester United Patrice Evra suna kallon juna a lokacin wasan Premier a filin wasa na Anfield. lokacin da Evra yace Suarez ya zage shi REUTERS/Phil Nobl/Files

A Gobe Assabar akwai wasa tsakanin Manchester United da Liverpool a Old Trafford, wasan da zata kwashi ‘yan kallo tsakanin Luiz Suarez na Liverpool da Patrice Evra da United. Wannan ne dai karo na farko da Suarez zai buga wasa da United bayan haramta masa buga wasanni Takwas.

Talla

A gasar FA Liverpool ta samu galabar United ci 2-1 a Anfield makwanni biyu da suka gabata, ba tare da suarez ba, amma kocin Liverpool Kenny Dalglish yace sun umurci Suarez hada hannu da Evra a wasan gobe.

Idan dai United ta samu nasara a gobe, zai kasance tana saman Tabur da maki daya tsakaninta da Manchester City wacce zata bakunci Aston Villa a Ranar Lahadi bayan ta doke Fulham ci 3-0 a karshen makon jiya.

A karshen mako akwai wasa tsakanin

Everton da Chelsea,

Sunderland da Arsenal

Tottenham da Newcastle
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.