Kwallon Kafa

Barcelona da Chelsea sun sha kashi, Mancini zai dawo da Tevez, Suarez ya nemi gafara

Dan wasan Manchester United Patirce Evra lokacin da yake murnar lashe wasa kusa da suarez na liverpool a filin wasa na Old Trafford inda Manchester ta doke Liverpool ci 2-1
Dan wasan Manchester United Patirce Evra lokacin da yake murnar lashe wasa kusa da suarez na liverpool a filin wasa na Old Trafford inda Manchester ta doke Liverpool ci 2-1 REUTERS/Darren Staples

Barcelona da Chelsea sun sha kashi, Suarez kuma ya nemi gafara bayan kin hada hannu da Evra a wasan da Liverpool ta sha kashi hannun Manchester United ci 2-1. Roberto Mancini na Manchester City yace zai hada hannu da Tevez idan har ya nemi gafara.

Talla

Spain

A La liga a spain yanzu maki 10 ne tsakanin Real Madrid da Barcelona, bayan Barcelona ta sha kashi hannun Osasuna ci 3-2. Cristiano Ronaldo kuma ya zira kwallaye uku a ragar Lavente inda aka tashi wasan ci 4-2.

Sau shida ke nan Cristaino na zira kwallo uku a raga a kakar wasan bana.

Pep Guardiola Kocin Barcelona ya kariya, yace ya hakura da La liga amma zai yi kokarin kare kofin shi na Champions league.

Saboda Champion league ne Pep Guardiola ya ajiye zaratan ‘Yan wasan shi Xavi Hernandez da Andres Iniesta da Cesc Fabregas a saman Benci inda zai bakunci kasar Jamus a ranar Talata domin karawa da Bayern Leverkusen.

Ingila

A Ingila, Luiz Suarez na Liverpool ya nemi gafarar Patrice Evra na Manchester United bayan kin hada hannu da shi a wasan da Liverpool ta sha kashi hannun United ci 2-1.

Rashin gaisawa da Evra a wasan farko bayan haramta masa buga wasanni 8 ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a harakar kwallon kafa a ingila, inda shugaban kungiyar kwararrun ‘yan wasa Gordon Taylor yace hakan bai dace ba ga Suarez, Sir alex Ferguson kuma na Manchester ya nemi Liverpool ta sallami Suarez.

Amma a shafin Liverpool na Intanet, Suarez yace ya zanta da kocin shi Kenny Dalglish tun lokacin da al’amarin ya fara ukuwa a Old Trafford, a cewarsa ya yi kuskure tare da yin nadama.

Yanzu haka dai Manchester City ce ke ci gaba da jagorancin Table bayan ta doke Aston Villa ci 1-0 a ranar Lahadi.

Kocin Chelsea kuma Andre Villas-Boas ya amsa shan kashi hannun Everton, daruruwan magoya bayan Chelsea ne suka dinga yi masa sowa tare da bayyana cewa bai san abinda yake yi ba bayan sun sha kashi hannun Everton ci 2-0 a filin wasa na Goodison Park.

Yanzu haka dai Chelsea tana matsayi na biyar ne a saman Tebur.

Dan wasan Najeriya Peter Odemwingie ya zira kwallaye uku a raga inda kungiyar shi ta west Bromwich Albion ta lallasa Wolve ci 5-1. Sunderland kuma ta sha kashi ne hannun Arsenal 1-2.

Kocin Manchester City manager Roberto Mancini yace zai hada hannu da Tevez tare da amincewa da shi a tawagar City idan har dan wasan ya nemi gafarar shi.

Faransa

A faransa kuma Paris Saint-Germain ta dare saman Table bayan an tashi wasa babu ci tsakaninta da Nice, inda kuma Bordeaux ta lallasa Lille ci 5-4.

Carlo Ancelotti yace yana fatar lashe kofin gasar, sai dai a mako mai zuwa ne PSG zata fafata da Montpellier da ke bi mata a Tebur da tserayyar maki daya.

Jamus

A Bundeliga ta kasar Jamus Mario Gomez na Bayern Munich yace suna bukatar matsala ta abkawa Borussia Dortmund idan har suna bukatar lashe kofin kasar.

Gomez ne dai ya zira kwallaye biyu a ragar Kaiserslautern a Munich a ranar Assabar, wanda ya basu damar kasancewa matsayi na biyu a Saman Tebur, amma yace suna fatar wata kaddara ta abkawa Dortmund.

Maki biyu ne dai tsakanin Bayern munich da Dortmund.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.