Zambia

Zambia ta lashe kofin Afrika

'Yan wasan kasar Zambia lokacin da suke lashe kofin gasar cin kofin Afrika na bana.
'Yan wasan kasar Zambia lokacin da suke lashe kofin gasar cin kofin Afrika na bana. REUTERS/Thomas Mukoya

Kasar Zambiya ta lashe gasar cin kofin Afrika  bayan doke Cote d'Ivoire ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wannan ne karo na farko da Zambia ta samu nasarar lashe kofin gasar bayan zuwa na biyu a shekarar 1974 da 1994.

Talla

Wasan karshen bata yi wa kasar Cote d’IVoire dadi ba domin tun fara gasar ba a samu galabarta ba sai a jiya. Gervinho na Arsenal da Kolo Toure ne suka barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda ya bai wa Zambia nasara bayan Drogba ya barar da kwallo ana cikin wasa.

Wannan rana ce ta farin ciki ga Zambiya musamman saboda ‘yan uwansu da suka mutu a hadarin jirgin sama a kasar Gabon a shekarar 1993.

Tun da farko dai kasar Zambia ce ta haramtawa kasar Ghana buga wasan karshe bayan doke Senegal da Tunisia da Morocco a zagayen farko.

Wasan karshen dai ta samu halartar masu ruwa da tsaki a harakar kwallon kafa a duniya musamman Sepp Blatter Shugaban hukumar FIFA da Michel Platini shugaban hukumar kwallon kafar Turai, da kuma shugaban kasar Cote d’Ivoire Allasane Ouattara da ali Bongo na Gabon da Shugaban kasar Equatorial Guinea.

Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda yana cikin wadanda suka kai ziyara Gabon a wasan karshe domin nuna goyon bayan shi ga ‘yan wasan Copper Bullet wanda ya kwashe tsawon shekaru 27 yana shugabancin Zambia kuma a lokacin shi ne ake wa ‘yan wasan Zambia da lakabin KK 11.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.